Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
…
continue reading
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
…
continue reading
Satu-satunya Ambisi Kita adalah Kebebasan!
…
continue reading
Disini kita akan bahasa isu-isu anak muda yang sedang booming!
…
continue reading
Podcast berisi interview dengan narasumber-narasumber yang bercerita soal perspektif kehidupan mereka. Perspektif yang disorot, mulai dari profesi, pribadi, sampai nilai-nilai tertentu.
…
continue reading
Mungkin kita sedang berada di situasi yang sama dan akhirnya dipertemukan di titik ini
…
continue reading
Halo kengkawans. Di Podcast ini, Anan dan Hasby bakal cerita seputar pengalaman liputan peristiwa yang lagi in. Kita berdua si buruh media ini, bakal bacotin sejumlah fenomena berdasarkan pengalaman liputan kita. Pastinya, buat kasih input positif dengan cara yang seger meski kadang unfaedah. Hehe Jangan lupa falaw ig @anansurya dan @hsbyallh yaa.. Dengerinnya jangan serius serius lhoo.. Wkwk
…
continue reading
Podcast sok serius tentang opini Azriel dan Grego mengenai suatu permasalahan atau objek yang menjadi concern dalam kehidupan sehari-hari. (kritik&saran:[email protected]) Support this podcast: https://podcasters.spotify.com/pod/show/BRAINWASHED/support
…
continue reading
Bukan lagi soal eksistensi atau popularitas, tapi di sini kita siap menemani kalean, mengubah obrolan berat jadi ringan jika ditimbang dengan satuan kilogram. Berlandaskan asas santai, chill, tapi GAYENG. Menyatulah bersama kami di Podcast Bango! Support this podcast: https://podcasters.spotify.com/pod/show/bangngobrol/support
…
continue reading
Hobi bicara film, Bola, atau hal absurd lainnya. Cover art photo provided by Alex Rodríguez Santibáñez on Unsplash: https://unsplash.com/@alexrds
…
continue reading

1
Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin Sallah
26:36
26:36
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
26:36A duk lokacin da aka ce lokutan bukukuwa sun karato, akan samu sauyi a dukkan alamura. Daya daga cikin irin wadannan sauyi da ake samu shine na farashin kayayyakin masarufi. A wasu lokuta, akan samu tashin farashin irin wadannan kayayyaki, a wasu lokutan kuma akasin haka. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai tattauna ne kan farashin kayayyakin ma…
…
continue reading

1
Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Kasa Kiranye
30:12
30:12
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
30:12Send us a text Mulkin demokradiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin dan adam. A lokacin da ta baka damar tsayawa don a zabe ka kan wani mukami, kazalika ta baka damar zaben wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka. Wani abun da demokradiyyar ta baiwa alumma dama a kai kuma shine na yin kiranye ga wakilan da suka zaba musamman idan wadan…
…
continue reading

1
Yadda Kasuwanci Ke Kasancewa Gabani Da Cikin Ramadana
22:17
22:17
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
22:17Send us a text Hausawa sunyi gaskiya da suka ce ‘yawan mutane sune kasuwa’. Yawan hada hadar da ake yi tsakanin ‘yan kasuwa da abokan cinikin su na daya daga cikin abun da zai tabbatar maka kasuwanci na gudana kamar yadda ake so. Sai dai da Zarar ance watan Ramadana ya kama wasu daga cikin kasuwanci kan samu nakasu, inda wasu kuma ke samun habbaka.…
…
continue reading

1
Illar Sare Itatuwa Ga Canjin Yanayi Da Lafiyar Mu
30:13
30:13
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
30:13Send us a text Shekaru da dama kenan da hukumomin duniya ke gudanar da tarurruka da dama kan zakulo hanyoyin da za a kawo karshen dumamar yanayi a duniya. Dumama ko canjin yanayi na cigaba da barazana ga duniya, inda ake samun sauye sauye ga yanayi da wasu abubuwa da masana ke bayyana ka iya kara ta’azzara in ba’ayi wani abu a kai ba. Daya daga cik…
…
continue reading

1
Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari
23:03
23:03
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
23:03Send us a text Sana’a na taka muhimmiyar rawa wajen habbaka tattalin arzikin alumma. Alumma da dama musamman a wannan lokacin na kara bayyana alfanun koyan sana’ar hannu don dogaro da kai maimakon dogara da aikin gwamnati ko na kamfani. Sai dai ana zargin wasu masu sana’ar hannu da rashin cika alkawari a wurin sana’ar su. Irin wadannan masu sana’ar…
…
continue reading

1
Abin Da Kundin Tsarin Mulki Ya Ce A Kan Ayyana Dokar Ta Ɓaci
27:18
27:18
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
27:18A karshe dai hasashen da wasu ke yi a Ribas ya tabbata, inda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci, ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa, da ma ''yan majalisar dokokin jihar. Sai dai bayan ayyana wannan doka da shugaban kasar ya yi 'yan Najeriya da dama suna ta bayyana ra’ayoyinsu kan wannan lamari. Yayin da wasu suke …
…
continue reading

1
Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan
27:23
27:23
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
27:23Send us a text Mallakan Muhalli na daya daga cikin burin kowanne dan Najeriya. Sai dai wannan buri a mafi yawan lokacin baya cika musamman ga masu matsakaitan samu. Kananan ma’aikata da mafi karancin albashin su yake naira dubu saba’in ba zai ciyar dasu, ko tufatar dasu ba, ballantana har suyi tunanin mallakan muhalli nasu na kashin kansu. Sai dai …
…
continue reading

1
Guraben Aiki Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya
23:50
23:50
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
23:50Send us a text Duk da kukan rashin aikin yi da ako da yaushe ke cigaba da addabar ‘yan Najeriya, a wasu lokutan ba rashin aikin yi ne matsalar ba, wadanda zasu cike guraben ayyukan ne suka yi karanci a Najeriya. Alkaluma na cigaba da bayyana dubban ‘yan Najeriya ne dai ke fito wa daga manyan makarantun kasar a kowace shekara. A yayin da da yawa bas…
…
continue reading

1
Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya
25:31
25:31
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
25:31Send us a text Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi. Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika b…
…
continue reading

1
Ko Yarjejeniya Da ’Yan Ta’adda Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Arewa?
27:15
27:15
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
27:15Send us a text Masu iya magana kan ce dole uwar na ki. Matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa musamman a Arewacin Najeriya tana tilasta wa wasu al’ummomi zakulo hanyoyin samun sa’ida ko yaya suke. Daya daga cikin wadannan hanyoyi da wasu al’ummomi suka runguma ita ce kulla yarjejeniya da ’yan bindigar dake addabar yankunansu. Shin ko cimma yarjej…
…
continue reading

1
Ko Kun San Asalin Tashe Da Tarihinsa A Kasar Hausa?
27:42
27:42
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
27:42Bayan dunbum falala, da yawan samuwar ibadun dake kara kusanta bayi ga ubangijin su, da azumin watan ramadana ke zuwa dashi kamar yadda malamai suka saba fada mana, Hakazalika Kuma a watan na Ramadan dai na zuwa da wata alada mai dimbin tarihi dake debe wa alumma musamman na arewacin Najeriya kewa. Wannan aladar itace ta tashe da ake fara yinta da …
…
continue reading

1
Abubuwan Da Suke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya
21:42
21:42
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
21:42Send us a text Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da daukar dumi yayin da ’yan kasa da dama suka yi kasake suna jiran girgiza ta gaba wadda wasu suke ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya diga mata dan ba. A baya-bayan nan dai an yi ta tsegunguma da rade-radi a kana bin da wasu jiga-jigan ’yan siyasar kasar nan, musamman ’yan ad…
…
continue reading

1
Ladan Da Mai Aikin Karfi Yake Samu A Lokacin Azumi
25:59
25:59
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
25:59Send us a text Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki. Sai dai a lokacin da wadannan mutane suke samun rangwame, akwai wadanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu. Sau da dama irin wadannan mutane sai sun fita sun yi aiki a…
…
continue reading

1
Falalar Bude Baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi
26:50
26:50
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
26:50Send us a text Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yake kara dankon zumunci da kaunar juna da albarka a tsakanin al’umma. Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu Karin kusanci da shakuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci. Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da tare da iyalin su al’ada. Shin ko m…
…
continue reading

1
Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba?
20:26
20:26
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
20:26Send us a text Fiye da wata guda ke nan tun bayan da Matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita. Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa wato NNPCL ya sanar da rage nasa farashin. Sai dai har yanzu ba a ga ragin a gidajen mai ba. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi na…
…
continue reading

1
Yadda Zawarawa Suke Dandana Kuda A Watan Ramadana
31:09
31:09
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
31:09Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale – ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza shiryawa. Wani rukunin wadannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a k…
…
continue reading

1
Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar Da ‘Ramadan Basket’ Ba
20:57
20:57
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
20:57Send us a text A aladance, a duk lokacin da aka ce watan Ramadana ya karato samari da ‘yan mata kan yi musayar kyaututtuka don kyautata wa abokan zaman su. Misali, a lokacin azumi samari kan sayi kayan bude baki da suka hada da madara, kwai, da sauran kayan makulashe wanda ake yiwa lakabi da ‘’Ramadan Basket’’ a turance don kaiwa ‘yan matan su. Sai…
…
continue reading

1
Yadda za ku yi girke-girken Azumi da kuɗi kaɗan
14:49
14:49
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
14:49Send us a text Yanayin tsadar rayuwa da ake ciki ya sa dole a yi tattalin kudin da ake kashewa. An saba da Ramadana ana yawan yin girke-girke da kayan buda baki iri-iri, amma kuma wannan azumin ya zo cikin yanayi na matsin tattalin arziki. Shirin Najeriya a Yau ya duba hanyoyin da za ku yi girke-girken da yawa yadda aka saba cikin sauki ba tare da …
…
continue reading

1
Ko Kun San Azumi Na Inganta Lafiyar Jiki?
42:18
42:18
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
42:18Send us a text Alumma na yin azumi ne bisa dalilan addini don samun lada kamar yadda Allah ya umurta a cikin Qurani mai girma. Sai dai daga baya binciken masana kimiyya ya gano cewa bayan lada da ake samu daga yin azumi, akwai wasu alfanu da mai azumi ke samu ga lafiyar jikin shi da suka hada da inganta karfi da zurfin tunani zuwa fitar da gurbatat…
…
continue reading

1
Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa
22:58
22:58
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
22:58Send us a text Wutan lantarki a Najeriya ya zama ginshikin rayuwa da alumma basa iya rayuwa ba tare dashi ba. A duk lokacin da aka ce an dauke shi zaka ga yadda alumma kan shiga cikin matsanancin hali, wasu da dama sun ta’allaka ne dashi wajen tafiyar da harkokin su na yau da kullum, kai har ma da kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkw…
…
continue reading

1
Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa
23:12
23:12
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
23:12A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A al’adance, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son …
…
continue reading

1
Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi?
26:29
26:29
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
26:29Send us a text Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa? Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl? Yayin da ake shirye-shiryen tarbar watan Ramadana, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nau’ukan dabino da alfanunsa ga dan’Adam, musamman mai azumi.Oleh Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
…
continue reading

1
Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri
19:39
19:39
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
19:39Send us a text Cutar kyandar biri da aka fi sani da Mpox ta kara bulla a Najeriya. Na baya bayan nan shine wanda ta bulla a jihar Filato inda aka samu wadanda suka kamu da ita mutum 11 da sai wanda ya rasa ransa mutum daya. Cutar ta kyandar biri ta bulla ne a kananan hukumomi biyar da suka hada da Jos ta Arewa, Bokkos, Shendam, Mangu da kuma Kenke.…
…
continue reading

1
Dalilan Da Ba Zamu Sauke Farashin Burodi Ba
29:51
29:51
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
29:51Send us a text A daidai lokacin da wasu alumma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci a kasuwanni kamar su shinkafa, masara da sauran kayan hatsi. Shima farashin flawa da ake amfani dashi wajen sarrafa biredi, gurasa da sauran makulashe ya sauka a kasuwa. Sai dai duk da saukar da farashin flawar tayi, alumma na cigaba da kokawa kan yadda har y…
…
continue reading

1
Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano
27:50
27:50
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
27:50Send us a text Tun bayan bayyana kafa Gwamnatin Bibiya ko kuma Shadow government a turance da wata kungiya karkashin jamiyyar APC a jihar kano tace zata yi ne ne dai alumma da dama keta jefa ayar tambaya kan halascin wannan gwamnati. Kungiyar dai ta bayyana cewa zata kafa wannan gwamnati ne don bibiyan ayyukan gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf don …
…
continue reading

1
Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi?
22:33
22:33
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
22:33Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan …
…
continue reading

1
Cigaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Zasu Samar
22:17
22:17
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
22:17Send us a text A kwanakin baya ne dai shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kirkiri sabbin hukumomin shiyyoyin kasar nan da nufin kawo cigaba ga wadannan shiyyoyi. Gabanin kirkirar wadannan hukumomin, gwamnatin da ta gabata karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ce ta fara kirkirar hukumar raya yankin Neja Delta bayan wasu kalubal…
…
continue reading

1
Dalilan Saukar Farashin Kayan Masarufi A Kaswanni
26:08
26:08
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
26:08Send us a text Bayanai daga sassa daban-daban na Najeriya suna nuni da cewa farashin kyayyakin masarufi na ta faduwa a kasuwanni. Kafin hakan dai farashin ya yi ta tashi, har ya kai ga duk abin da mutum ya saya a yau, idan ya koma kasuwa bayan kwana biyu zai ji an ce ya tashi. Ko wadanne dalilai ne suka sa farashin kayayyakin masarufi suke ta sauka…
…
continue reading

1
Tasirin Da Kyauta Ke Dashi A Soyayya
24:42
24:42
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
24:42Send us a text A duk lokacin da aka ce soyayya ta kullu a tsakanin mutane biyu, hakan na tafe da wasu hidimomin da soyayyar ke zuwa dasu. Cikin irin wadannan hidimomi akwai kyauta da masoya ke baiwa junan su. Wadannan kyaututtuka sun hada da turare, agogon hannu, sarka ko zobe da dai sauransu.Oleh Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
…
continue reading

1
Kalubalen Dake Neman Durkushe Kafafen Rediyo A Arewa
28:15
28:15
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
28:15Send us a text Rediyo na daga cikin kafofin da alumma da dama suka dogara dasu don jin labarai, shirye shirye da kuma nishadi. Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa da alumma dama kai musamman duba da yadda aka bada shaidar cewa tafi kowace kafar media saurin yada bayanai ba a cikin birane ba, har ma da yankunan karkara. Sai dai a wannan ga…
…
continue reading

1
Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa
29:44
29:44
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
29:44Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa. Sai dai wannan dadaddiyar al’ada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan wannan al’ada da kuma dalilin gushewar ta.…
…
continue reading

1
Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya?
30:00
30:00
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
30:00Send us a text Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi …
…
continue reading

1
Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya?
25:12
25:12
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
25:12Send us a text A tsakanin al’umma akan karkasa mutane gida-gida a bisa mizani na tattalin arziki, musamman a tsarin jari-hujja: akwai mawadata, akwai matalauta. A tsakanin al’umma akwai aji na mutane masu matsakaicin samu wanda ake kira “Middle Class”. Akan saka mutane a wannan aji ne galibi bisa la’akari da aiki ko sana’ar da suke yi, da kudin da …
…
continue reading

1
Dalilin Faduwar Farashin Tumatur A Kasuwa
27:44
27:44
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
27:44Send us a text Shin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwar a kasuwa? Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin Tumatur yayi tashin gwauron zabo wanda aka dade ba’a ga irin sa ba. A wancan lokacin, sai da farashin tumaturin ya kai ga iyalai da dama sun hakura dashi sun koma sayen na gwangwani ko na leda. Wannan ne batun da shirin Najeriy…
…
continue reading

1
Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata
25:44
25:44
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
25:44Send us a text A tsakanin Hausawa akan yi wa jaririya wani nau’i na kaciyar mata, wanda ake kira yankan angurya, kwana bakwai da haihuwarta. Ko menene alfanu ko illar wannan al’ada ga ’ya’ya mata? Albarkacin Ranar Yaki da Kaciyar Mata ta Duniya, shirin Najeriya A Yau zai yi nazari a kan wannan al’ada da tasirinta a rayuwar mata.…
…
continue reading

1
Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma 'Event Centre'
29:48
29:48
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
29:48A da akan kwashe kwanaki ana bukuwan aure a kasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin bik da zaman ajo zuwa budar kai da sayen baki. Sai dai wadannan al’adu sannu a hankali suna ta gushewa. Ko mene ne dalilin wannan sauyin? Wannan ne batun da shirin Daga Laraba zai duba a wannan makon.Oleh Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
…
continue reading

1
Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kudi Da Yawa Ba
27:04
27:04
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
27:04Send us a text Mutanen dake da sha’awar shiga harkar noma kodai don sama wa kansu abin da za su ci ko kuma don samun kudaden shiga na fuskantar kalubale. Wannan kalubale ya hada da karancin ilimin noman, da na irin shuka, da rashin gonaki da dai sauran su. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan batu tare da samar da hany…
…
continue reading

1
Dalilan Da Suka Sa Zamu Kashe Naira Biliyan Biyu Da Rabi Kan Auratayya A Kano
25:08
25:08
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
25:08Send us a text Tun bayan da jihar kano ta fitar da rahoton ware zunzurutun kudi har naira biliyan biyu da rabi don auratar da marasa aure a jihar ne dai batun ke ta shan suka daga bangarori daban daban a fadin Najeriya. Wasu na ganin jihar na da wasu bukatun da suka fi auratar da alumma muhimmanci da ya kamata ace gwamnatin ta mayar da hankali a ka…
…
continue reading

1
Anya Jam’iyyar PDP Za Ta Kai Labari A Fagen Siyasar Najeriya Kuwa?
29:27
29:27
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
29:27Send us a text Shin shure-shure PDP take yi da ba ya hana mutuwa, ko kuwa motsi ne na alamun samun lafiya? Wannan ce tambayar da wasu ’yan Najeriya suke yi game da fito-na-fito da shugabannin jam’iyyar suka jima suna yi da juna. Tuni wasu ma suka fara diga ayar tambaya a kan makomar jam’iyyar bisa la’akari da tarin rikice-rikicen da suka dabaibaye …
…
continue reading

1
Hakikanin Dalilan Takaddama Kan Kafa Kotunan Shari’ar Musulunci A Kudu
22:52
22:52
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
22:52Send us a text Ana ci gaba da zazzafar muhawara a shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya a kan batun samar da kotunan Shari’ar Musulunci. Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a yankin ce dai ta buƙaci hakan. Sai dai wasu ƙungiyoyi da ma ɗaiɗakun mutane a yankin suna adawa da wannan buƙata. Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lok…
…
continue reading

1
Dalilan Da Suka Sa Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata
29:49
29:49
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
29:49Son haihuwar ‘ya’ya maza fiye da ‘ya’ya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin alummomi daban-daban. A tsakanin wasu al’ummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cika bai wa haihuwar ‘ya mace irin wannan muhimmancin ba. Ko wadanne dalilai ne suka sa wasu mutane suka fi son samu…
…
continue reading

1
Dabarun Noma Don Samun Kuɗaɗen Shiga
24:03
24:03
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
24:03Send us a text Akan ce “Noma tushen arziki”. Mutane da dama za su iya bayar da labarin da ke tabbatar da hakan; domin kuwa ko ba komai idan mutum ya samu abinci ya ci ya koshi babban arziki ne. Wasu ’yan Najeriya kan shuka kayan abinci a unguwannin su don sama wa kan su abincin da za su ci. Sai dai masana na ganin da wadannan mutane za su inganta w…
…
continue reading

1
Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Hanyar Intanet
29:34
29:34
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
29:34Send us a text Ci gaban zamani ya zo da sauye-sauye da dama a fannonin rayuwa daban-daban ciki har da kasuwanci. A yanzu hanyar sadarwa ta zamani, ko intanet, tana taka muhimmiyar rawa wajen tallata haja ko saye da sayarwa da banarori da dama. Tuni ’yan Najeriya da dama suka yi balaguro suka koma intanet da kasuwancinsu. Shrin Najeriya a Yau na wan…
…
continue reading

1
Matakan Samun Abinci A Kan Farashi Mai Rahusa A Najeriya
20:51
20:51
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
20:51Send us a text Wadatar da al’umma da abinci abu ne mai matukar muhimmanci ga duk ƙasar dake son zama lafiya cigaba. Sai dai a Najeriya cimma wannan buri na cin karo da ƙalubale, kama daga sauyin yanayi zuwa ambaliyar ruwa, daga rashin tsaro zuwa karancin zuba jari a bangaren noma. Rahotanni sun nuna cewa adadin abincin da aka samar bai kai yadda ya…
…
continue reading

1
Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓɓaka Tattalin Arzikin Najeriya
22:04
22:04
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
22:04Send us a text Kudaden crypto na cikin hanyoyin da zamani ya zo da su da nufin sauƙaƙa hada-hada a tsakanin alumma, musamman a ƙasashen da suka ci gaba. Sai dai a Najeriya, har yanzu ba kowa ne ya san wannan harka da kuma yadda ya kamata a yi ta ba, musamman duba da yadda kudin na crypto ya yi daraja a fadin duniya. Shirin Najeriya a Yau na wannan …
…
continue reading

1
Me Ya Sa Matasa Ba Sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana'a?
26:56
26:56
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
26:56Samun ingattattun malamai a makarantun firamare da sakandare na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tubalin ingantaccen kuma nagartaccen ilimi a cikin al’umma. Ɗorewar wannan fafutuka ta samar da ingantaccen ilimi kuma ta dogara ne a kan samun haziƙan matasa da za su maye gurbin malaman da ake da su yanzu. Sai dai a Najeriya, alamu suna nuni da yad…
…
continue reading

1
Yadda Kuɗin Kujera Yake Neman Hana Maniyyata Sauke Farali
25:27
25:27
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
25:27Send us a text Yanzu haka, saura mako biyu wa’adin da aka deba wa maniyyata Hajjin bana su biya kudin kujerar ya cika, amma rahotanni daga wasu sassan kasar nan na nuna cewa kalilan ne suka iya biyan. Kudin kujerar hajjin ya tsorata ’yan Najeriya a bana, bayan da hukumomi suka ce duk mai sha’awar sauke farali sai ya biya zunzuruntun kudi sama da Na…
…
continue reading

1
Yadda Rashin Ɗaukar Darasi Ya Haddasa Gagarumin Asara A Suleja
25:40
25:40
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
25:40Send us a text Ƙiyasi ya nuna cewa an yi asarar miliyoyin Naira bayan da shaguna makare da kayayyaki da motocin hawa da na haya suka ƙone ƙurmus, uwa uba kuma rayuka aƙalla 80 suka salwanta sakamakon fashewar tankar mai a Marabar Dikko da ke kusa Suleja a Jihar Neja. Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da faɗuwar tanka ta haddasa asarar dukiya da…
…
continue reading

1
Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo
25:45
25:45
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
25:45Send us a text A kwanakin baya farashin tumatir yayi tashin gwauron zabo a kasuwani, bayan watanni kadan kuma albasa ta tsefe kai. Ana cikin jimamin tashin farashin albasar ne sai ga na itta ya zabura. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan abubuwan da suka sa farashin citta ya yi tashin gwauron zabo a kasuwanni.…
…
continue reading

1
Yadda Birnin Abuja Ya Zama Yanki Mai Hatsari Ta Fuskar Tsaro
28:04
28:04
Main Kemudian
Main Kemudian
Senarai
Suka
Disukai
28:04Send us a text Rashin tsaro na ci gaba da addabar ’yan Najeriya a matakai daban-daban, a sassan kasar nan daban-daban. Yayin da a wasu yankuna ake fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya, a Abuja ana fama ne da masu kwacen motoci, da ’yan damfara, da sauran su. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wurare…
…
continue reading