"Shekara 8 Ina Tara Kuɗin Hajji Amma Yanzu Dole Na Fasa Zuwa"
Manage episode 408902167 series 3311743
Za a iya cewa aikin Hajji a Najeriya sai ga mai rabo, domin tun bayan bullar labarin hukumar alhazan Najeriya NAHCON na cewa an yi ɗori kan kudin da aka ware a baya ake ta ƙorafi.
Tuni wasu maniyyatan suka ce sun cire rai a yanzu, amma kuma hukumar ta ce akwai dalilan da babu yadda ta iya da su ne.
Shirin Najeriya a Yau ya duba matakin, da wasu suka ce yana neman hana talakan Najeriya zuwa aikin Hajji.
714 episod