Aminiya awam
[search 0]
lebih
Download the App!
show episodes
 
Artwork

1
Daga Laraba

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Unsubscribe
Unsubscribe
Mingguan
 
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
  continue reading
 
Loading …
show series
 
Tururuwar da mutane suke yi zuwa manyan biranen Najeriya na barazana ga wadannan alƙaryu ta fuskar tsaftar muhalli. Misali, wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa a duk sa'a daya birnin Legas kan yi baƙi 77 – hakan kuma kan haddasa karuwar sharar da ake zubarwa. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan yadda shara ke adda…
  continue reading
 
A karshe dai an ayyana John Mahama a matsayin zababben shugaban kasar Ghana bayan da al’ummar kasar sun yanke shawarar zabensa lokacin da suka kada kuri’a ranar Asabar din da ta gabata. Duk da sauran ‘yan Takara da John Mahama ya kara da su, ciki harda mataimakin shugaban kasar mai ci a yanzu wato Mahamudu Bawumia Musulmi na farko da ya tsaya takar…
  continue reading
 
Kishin kasa na cikin abubuwan da shugabanni, da sauran masu ruwa da tsaki suke kira ga ’yan Najeriya a kullum a kansu. Muhimmancin kishin kasa ga cigaban al’umma, musamman a kasa mai kabilu da addinai daban-daban irin Najeriya, abu ne da ba zai misaltu ba. Sai dai alamu na nuna cewa yan Najeriya sun fi nuna kishin kabilun da suka fito idan aka kwat…
  continue reading
 
Matsalar tsaro na daga cikin batutuwan da suka hana kasar nan cikas a ‘yan shekarun nan. Kuma kamar yadda alumma ke bayyanawa akwai karancin jami’an tsaro da ya kamata ace suna lura, tare da kiyaye rayuka da dukiyoyin alumma a koda yaushe. Karancin jami’an tsaron ne ya sa wasu daga cikin jihohin da rashin tsaron yafi kamari suka samar da wasu jami’…
  continue reading
 
An daɗe ana muhawara, musamman a Arewacin Najeriya, a kan buƙatar yin garambawul ga tsarin makarantun tsangaya. A baya dai waɗannan makarantu kan samar da mahaddata alqur’ani waɗanda kuma sukan dogara da kai Sai dai a wannan zamani, yaran da suke karatu a ƙarƙashin tsarin sun zama mabarata. Gwamnatoci da dama dai sun yi kokarin yin garambawul ga ya…
  continue reading
 
A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci. Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri bay a bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan za…
  continue reading
 
Kalmar almajiri ta samo asali ne daga yaren larabci wato almuhajir, dake nufin wanda ya bar garin sa don zuwa wani gari neman ilimi. Mafi yawan alummar arewa inda akafi sanin Kalmar sun taso ne sun ga ana gudanar da karatun allo ko almajirci, wanda hakan ke nufin almajirci ya samo asali ne tun lokacin da musulunci ya fara shigowa Najeriya daga gari…
  continue reading
 
Taron da Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta yi a Kaduna ya bar baya da kuria’a. Daya daga cikin shawarwarin da gwamnonin suka yanke ita ce ta kin amincewa da wani Kuduri da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai Majalisar Dokoki ta Kasa. Shin kishin Arewa ne ya sa gwamnonin suka yi Allah-wadai da Kudurin ko kuma son zuciya? Wannan ce muhawarar da ta…
  continue reading
 
Tarbiyya kamar yadda aka san ta a al’adance tana inganta ne idan al’umma gaba daya ta hada hannu wajen ladabtar da yara. Duk wanda ya kai shekaru talatin zuwa sama ya san cewa a da can iyaye da sauran jama’ar gari suna iya daukar tsumagiya don ladabtar da shi idan ya kauce hanya. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne kan alfanun ko illar…
  continue reading
 
Afrika na da dadadden tarihin girmama na gaba, musamman dattawan da ke cikin al’umma. Sai dai a wannan zamani akan samu matashi ya shafa wa idonsa toka ya fito bainar jama’a yana musayar zafafan kalamai da sa’o’in mahaifinsa. Shin me ya sa ake samun irin wannan? Don jin amsar wannan tambaya da ma wasu sai ku biyo mu a cikin shirin Daga Laraba na wa…
  continue reading
 
Sau da yawa akan samu rashin fahimtar juna a duk lokacin da wata mu’amala ta haɗa mata. Misali, a asibiti wajen haihuwa mata sun sha kokawa da yadda suke ce ’yan uwansu suna nuna musu rashin tausayi. Shirin Daga Laraba zai tattauna a kan wannan lamari, ya kuma auna shi a kan mizanin magamar da matan kan yi cewa “Ciwon ’ya mace na ’ya mace ne”.…
  continue reading
 
Wata muhawara da ta karade shafukan sada zumunta a kwanakin nan ita ce ko ’yan Arewa, musamman Hausawa, suna fita kasashen waje. Duk da wannan ba wani sabon abu ba ne, batun ya dauki sabon salo ne a shafukan sada zumunta, musamman Facebook da TikTok, inda ’yan kudancin Najeriya suke wallafa fayafayen bidiyo suna tambayar: shin Hausawa suna zuwa kas…
  continue reading
 
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan …
  continue reading
 
Sama da mako guda ke nan bayan komawa makarantu domin fara sabon zangon karatu a kusan dukkanin sassan Najeriya. Sai dai rahotanni sun yi nuni da cewa, ana samun karancin komawar dalibai makaranta a wasu sassan kasar. Shirin Daga Laraba na wananan makon zai yi duba ne a kan dalilan faruwar hakan.Oleh Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
  continue reading
 
Dangantaka ko alaka a tsakanin Najeriya da China tana ƙara yaukaka, musamman a baya-bayan nan. Ko a kwanan nan, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci wata tawaga zuwa kasar ta China domin halartar taron kyautata alakar kasuwanci tsakaninta da kasashen Afirka. Shirin Daga Laraba na wananan mako zai tattauna a kan ko mecece ribar ’yan Najeriya…
  continue reading
 
A duk lokacin da dogon hutun zangon karatu na karshe ya kare, iyaye su kan kasance cikin taraddadin yadda zasu fuskanci komawar Yara makaranta, saboda dumbin bukatu da yanayin ke zuwa dasu. Shin, me ya kamata, iyaye da masu makantu su fi mayar da hankali a kai, musamman la'akari da irin yanayin tsadar kayayyaki da kuncin rayuwa da ake fama dasu a N…
  continue reading
 
Duk da cewa, a wuni daya ne ake bikin ta, amma muhimman al'adun Hausawa da ake tattaunawa game dasu a ranar Hausa Ta Duniya, suna da tasiri a rayuwar al'umma ta yau da Kullum. Wata dadaddiyar al'ada da aka san al'ummar Hausawa da ita, ita ce al'adar nan ta fito da Abinci daga gidajen makota, inda ake haduwa aci tare musamman ma a Kullum da daddare.…
  continue reading
 
Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 21 ga watan Agusta domin tunawa da wadanda ayyukan ta’addanci ya rutsa da su. A duk lokacin da mutum ya fada hannun ‘yan ta’adda ko rikicin ta’addanci ya rutsa da su, sukan dade cikin damuwa a ransu. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai tattauna kan wannan rana da abin da ya kamata a yiwa irin wadannan mutane.…
  continue reading
 
A Najeriya babban bankin kasa CBN ya bayar da wa’adi ga bankunan domin tara adadin wasu kudade a matsayin jarinsu ko kuma su hade guri daya da masu karamin karfi a bankuna. A halin yanzu wasu har sun fara hadewa da wasu bankunan, duk da yake ba sabon abu ba ne hadewar bankuna waje guda a Najeriya. To amma me ke faruwa indan bankunan suka hade? shin…
  continue reading
 
Gwamnati na fidda shafukan da ‘yan kasa za su iya neman bashi ko tallafi, a lokaci guda kuma masu zamba ta intanet na bullo da shafukan bogi domin yaudarar al’umma. Yana da kyau mutum ya iya tantance shafin da za a iya yi masa kuste musamman abin da ya shafi kudi. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi bayani kan yadda za ku tantance shafukan in…
  continue reading
 
Lokaci na tafiya kuma matasa na turjiya kan shirinsu na zanga-zanga, duk da matakan da gwamnati ke ta dauka. Ana ta kokarin ganin zanga-zangar ta yiwu cikin lumana, domin kauce wa rikidewa zuwa ta tarzoma. Shirin Daga Laraba zai tattauna kan hanyoyin da suka kamata gwamnati ta bi domin samun mafita kan zanga-zanga.…
  continue reading
 
A wannan yanayi na damina kusan kullum wuni ake yi ana tafka ruwan sama a wasu sassan Najeriya. Akwai masu sana’o’in da sai sun fita za a samu taro da sisi amma kuma babu hali. Shirin Daga Laraba zai tattauna lan dabarun da ya kamata masu sana’o’i su yi amfani da su domin ganin ruwan sama bai dagula musu lissafi ba.…
  continue reading
 
Tun bayan janye tallafin man fetur, gwamnati ke ta rarraba kayan abinci ga talakawa domin rage musu radadi. A wannan makon Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarin raba tirela 20 ga kowace jiha a Najeriya da Birnin Tarayya duk da wasu na wannan salo ba ya tasiri. Shirin Daga Laraba ya duba yadda tallafin abincin daga gwamnatin zai magance damuw…
  continue reading
 
Kusan ko wace damina sai hukumomi sun gargadi mazauna wasu yankuna game da yiwuwar samun ambaliyar ruwa. A bana ma Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi gargadin cewa jihohi kusan 31 za su fuskanci ambaliyar da rushewar gine-gine. Shirin Daga Laraba ya tattauna kan abin da ya kamata a yi domin kauce wa asara sakamakon ambaliya.…
  continue reading
 
Hawan Daushe al’ada ce ta sarakunan Kasar Hausa a lokacin bikin Sallah. A masarautar Zazzau a kan yi wannan hawa a ranar ukun Sallah da yamma, kuma yakan tara ‘yan Kallo daga wurare daban-daban ciki har da Kano. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai duba yadda aka yi hawan na bana da yadda ya samo asali musamman a masarautar Zazzau.…
  continue reading
 
A yanayi na rashin lafiya a kan ga wasu maza na tuburewa likita namiji ba zai duba musu iyali ba, musamman wajen haihuwa a asibitoci. Amma akwai matan da su ma a ganin su, kunya kan hana su sakin jiki likitoci maza su duba su. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi nazari a kan meyasa wasu basu yarda likita namiji ya duba matansu a asibiti.…
  continue reading
 
Najeriya ta cika shekara 25 cikin tsarin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Ana kan tsari ne na shugaban kasa mai cikakken iko tun daga 1999 a ranar 29 ga watan mayu, duk da yake an sauya bikin wannann rana zuwa 12 ga watan Yuni. Toh shin wane irin ci gaba ko akasin haka aka samu cikin wadannan shekaru 25? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tatt…
  continue reading
 
Mu’amalar farar hula da sojoji a Najeriya ta mutuntuwa ce wadda zarar aka hangi soja a cikin gari jiki har karkarwa yake. Sai dai a ‘yan kwanakin nan a iya cewa yadda labarai ke yawan fita game da yadda fararen hula ke yin tsaurin ido wajen takalar sojoji da fada yana karuwa. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da ya sa fararen hula ke k…
  continue reading
 
Yau Laraba rukunin farko na maniyyata Hajjin bana daga Najeriya za su tashi zuwa kasa mai tsarki Duk da matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan, akalla mutum sama da 50,000 ne ake sa ran za su sauke faralin daga Najeriya. Shin wane abu maniyyatan ya kamata su maida hankali a kai? NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Masu Gidajen Haya Suke Tsuga Kud…
  continue reading
 
Idan aka zagaya jami’o’i ana samun dalibai da dama wadanda ba su wuce shekara 15 ba a aji. A yanzu zamani ya sauya, abin ya zama Ruwan dare. Mai yiwuwa a lokacin da kuke makarantar firamare ko sakandare kun hadu da wadanda aka yiwa tsallaken aji, wato a bai wa dan aji 4 damar rubuta jarabawar kammala firamare ko kuma dan SS2 damar rubuta WAEC ya wu…
  continue reading
 
Yau ce ranar 1 ga watan Mayu da aka ware a Najeriya da wasu sassan duniya domin jinjina ga rawar da ma’aikata ke takawa wajen ci gaban kasa. Sai dai yayin da 'yan Najeriya da dama ke kuka da halin da aka shiga na ƙuncin rayuwa, ma'aikata na kan gaba wajen bayyana yadda suka ce suna tagayyara kuma aikin ba riba ta wani ɓangaren. Shirin Daga Laraba n…
  continue reading
 
Bayan komawa tsarin rukuni daban-daban na bayar da wutar lantarki Idan kamfanoni na neman afuwa to yawancin ga ‘yan rukunin farko ne. Wasu na ji a ransu kamar su ba kwastomomi bane ga kamfanonin domin kulawar da ake ba su ta nuna ba a tare da su. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da ya sa hankalin kamfanonin wutar lantarki ya karkata w…
  continue reading
 
A watan Ramadan sabbin ma'aurata na alfahari da azuminsu na farko a gidan aure. Shin mene ne abin da yake kayatar da gidan aure musamman a wannan lokaci na Ramadan? Ya ya kamata ma'aurata su kasance? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna yadda ma'aurata ke samun tabarruki da falala a yanayinsu na farko.…
  continue reading
 
I’itikafi sunna ce mai karfi a wannan lokaci, kuma jama’a masu sukunin shiga na kwashe kwanaki kusan goma a masallaci wajen ibada. To amma me ya kamata ku sani gameda shiga itikafi kuma wadanne abubuwa ake son mutum ya kiyaye a lokacin? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba matakan yin i'itikafi da abubuwan da ya kamata ku sani gameda hakan.…
  continue reading
 
A yayin da ake shiga goman tsakiya na watan Ramadan, malamai na kira ga al’umma da su dage wajen ibadu domin samun dacewa. A al’adance a wannan goma ta tsakiya akwai wasu al’adu musamman na tashe da kuma kirarin goma ta wuya bayan ta marmari. Shirin Daga Laraba ya yi tsokaci ne a kan wasu abubuwa da da ake yi a goman tsakiyar Ramadan a addinance da…
  continue reading
 
Mutane da dama sun shaida cewa takardar Nairar Najeriya na saurin lalacewa. Wasu na ganin masu liki a wajen bukukuwa da yadda ake kasuwancin sabbin kudi na taka rawa. Toh amma me ya kamata a yi, me kuma doka tace kan kudin da suka tsufa suka lalace. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba halin da mutum zai iya jefa kansa idan har aka same shi da…
  continue reading
 
Tsadar rayuwa ta sa ruwan leda wato 'fiyowata' ya fara zama abin tattaunawa gameda yadda yake tsada. Wasu na ganin shine ruwan da ake samu mai dama-dama wajen tsafta idan mutum na so ya sha ruwa, sai dai yadda yake kara tsada a sassa daban-daban na Najeriya ya sa ana komawa shan ruwa mara tsafta a wasu wuraren. Sai dai masu sarrafa ruwan na cewa ba…
  continue reading
 
Wannan rana ce majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ranar harshen uwa ta duniya. Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 40 cikin 100 na al’ummar duniya ba sa samun ingantaccen ilimi ne saboda rashin amfani da yarukansu na asali. Wasu harsuna na fuskantar barazanar shafewa a duniya saboda iyaye sun daina koyar da ’ya’yansu yadda za su yi magana d…
  continue reading
 
Ranar masoya kan dauki hankali a ranar 14 ga watan Fabreru, inda yawancin masoya ke kure malejin soyayyarsu. Amma akwai masu ganin ba lallai a samu soyayyar gasakiyaa yanzu ba. Sai dai ko kun san yadda aka yi wannan ta samo asali? Albarkacin ranar masoya Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba tasirin wannan rana da salsalar ta.…
  continue reading
 
Kafafen sada zumunta sun zama farfajiyar baje kolin basira, yayin da ta kan zame musu hanyar bayyana damuwa da share kokensu. Ana yawan buga misali da cewa an yiwa yankin Arewacin Najeriya nisa wajen samun tagomashin a soshiyal midiya. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba dabarun da masu amfani da shafukan za su bi wajen ganin sun amfana yadda…
  continue reading
 
A duk lokacin da ma’aikaci ya tsinci kanshi a ofishi mai matsin lamba da takura, masu sharhi na ganin aiki bai cika tafiya daidai ba. Wasu wuraren aiki na fuskantar matsin lamba daga oganni ko kuma tsarin aiki da zai sa a yi ta korafi. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba yadda wuraren aiki masu matsin lamba ke takura rayuwar ma’aikata da yadd…
  continue reading
 
Lafiya dai ita ce uwar jiki, babu mai fushi da ita. A yanayin da aka ciki babu mai son ya ga ya kwanta rashin lafiya, domin ana lallaba halin da ake ciki. Jama’a na kokawa a fannoni da dama yayinda wasu kyale batun ziyartar asibiti ko shan magani ko da sun ji alamar canji a jikinsu. Ku kasance da shirin Daga Laraba na wannan mako domin wasu dabarun…
  continue reading
 
Yanzu wata guda kenan tun bayan da sojoji suka yi kuskuren kai hari kan masu Maulidi a garin Tudun Biri dake jihar Kaduna. Harin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 100, inda hukumomi da gwamnati ba su yi wata-wata ba wajen daukar alhakin hakan da kuma bayyana cewa za a yi abin da ya dace wajen bin hakkin waɗanda lamarin ya shafa. Toh shin zuwa yanz…
  continue reading
 
Tasirin goro ga masu cinsa yana zama abu mai wahala mutum iya dainawa. Goro na da mahimmanci a Kudancin Najeriya musamman ga Kabilar Igbo. Haka ma yawanci dattawa a Arewacin Najeriya har ma matasa da mata a wasu lokutan suna cin goro, inda abin ya kan zame musu jiki, yayinda ake amfani da shi a wajen taruka na aure ko suna duk da ba a nomanshi a ya…
  continue reading
 
Loading …

Panduan Rujukan Pantas

Podcast Teratas