Bincike: Yadda Mayanka A Abuja Ke Samar Da Nama Mai Ƙazanta
Manage episode 401070217 series 3311743
Yana da kyau a kowane lokaci mu yi nazarin tsaftar naman da muke ci. Ta iya yiwuwa ba ku taɓa damuwa da sanin yadda ake sarrafa naman dabbobi a mahautu ba.
Za ku yi mamakin irin ƙazantar da bincikenmu ya banƙado ana yi da yaɗa cututtukan ga naman da mutane ke siya daga mahautu.
Shirin Najeriya a Yau ya maida hankali kan yadda wasu mahauta a birnin tarayya Abuja ke gudanar da aikinsu ba tare da tsafta kula da naman dake shiga gari ba.
716 episod