NE awam
[search 0]
lebih
Download the App!
show episodes
 
Artwork

1
Daga Laraba

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

icon
Unsubscribe
icon
Unsubscribe
Mingguan
 
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
  continue reading
 
Artwork

1
Najeriya a Yau

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

icon
Unsubscribe
icon
Unsubscribe
Mingguan+
 
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
  continue reading
 
Artwork
 
Tarihin Afrika ta hanyar zamanin manyan mutanen Nahiyar. Shirin na kunshe da sautin shugabannin Afrika da suka gabata da wadanda suka yi zamani da su. Babu wanda ke iya share tarihin wata al’umma, domin duk al’ummar da ba ta da tarihi kamar duniya ce babu rayuwa. Alain Foka ne ya gabatar da shirin daga RFI sashen Faransanci a Paris wanda aka fassara zuwa Hausa.
  continue reading
 
Artwork

1
Tanggal Merah

Taher dan Vega

icon
Unsubscribe
icon
Unsubscribe
Bulanan
 
Podcast dari @iqbaltaher & @astridvegs yang membahas cerita-cerita seru di balik perjalanan backpacking mereka berdua berkeliling dari satu tempat ke tempat lain. Selamat menikmati tanggal merah!
  continue reading
 
Artwork

1
Podcast Kamis Ceria

Podcast Kamis Ceria

icon
Unsubscribe
icon
Unsubscribe
Bulanan
 
Podcast Kamis Ceria Merupakan Podcast Comedy Yang membahas Tentang Fenomena Menarik Yang sedang Digandrung Oleh Muda - Mudi Negeri Ini. Podcast Ini Bertema Kan Obrolan waroeng Kopi Yang Obrolonya Terserah Kami.
  continue reading
 
Loading …
show series
 
Send us a text Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi …
  continue reading
 
Shirin na Tambaya da amsa na baiwa masana damar kawo ƙarin haske a wasu daga ciƙin tambayoyinku daga nan Rfi,shin ko wata kasa a doron duniyar nan, ta taba fusƙantar irin gobarar da ta tashi a birnin Los Angeles na Amurka kuma duk da kasancewarta babbar ƙasa mai isassun kayan aiki,ko mai ya hana ya hana Amurka samun nasarar shawo kan gobarar a ciki…
  continue reading
 
Send us a text A duk lokacin da aka ce soyayya ta kullu a tsakanin mutane biyu, hakan na tafe da wasu hidimomin da soyayyar ke zuwa dasu. Cikin irin wadannan hidimomi akwai kyauta da masoya ke baiwa junan su. Wadannan kyaututtuka sun hada da turare, agogon hannu, sarka ko zobe da dai sauransu.Oleh Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
  continue reading
 
Send us a text Rediyo na daga cikin kafofin da alumma da dama suka dogara dasu don jin labarai, shirye shirye da kuma nishadi. Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa da alumma dama kai musamman duba da yadda aka bada shaidar cewa tafi kowace kafar media saurin yada bayanai ba a cikin birane ba, har ma da yankunan karkara. Sai dai a wannan ga…
  continue reading
 
Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa. Sai dai wannan dadaddiyar al’ada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan wannan al’ada da kuma dalilin gushewar ta.…
  continue reading
 
Send us a text A tsakanin al’umma akan karkasa mutane gida-gida a bisa mizani na tattalin arziki, musamman a tsarin jari-hujja: akwai mawadata, akwai matalauta. A tsakanin al’umma akwai aji na mutane masu matsakaicin samu wanda ake kira “Middle Class”. Akan saka mutane a wannan aji ne galibi bisa la’akari da aiki ko sana’ar da suke yi, da kudin da …
  continue reading
 
Send us a text Shin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwar a kasuwa? Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin Tumatur yayi tashin gwauron zabo wanda aka dade ba’a ga irin sa ba. A wancan lokacin, sai da farashin tumaturin ya kai ga iyalai da dama sun hakura dashi sun koma sayen na gwangwani ko na leda. Wannan ne batun da shirin Najeriy…
  continue reading
 
Send us a text A tsakanin Hausawa akan yi wa jaririya wani nau’i na kaciyar mata, wanda ake kira yankan angurya, kwana bakwai da haihuwarta. Ko menene alfanu ko illar wannan al’ada ga ’ya’ya mata? Albarkacin Ranar Yaki da Kaciyar Mata ta Duniya, shirin Najeriya A Yau zai yi nazari a kan wannan al’ada da tasirinta a rayuwar mata.…
  continue reading
 
A da akan kwashe kwanaki ana bukuwan aure a kasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin bik da zaman ajo zuwa budar kai da sayen baki. Sai dai wadannan al’adu sannu a hankali suna ta gushewa. Ko mene ne dalilin wannan sauyin? Wannan ne batun da shirin Daga Laraba zai duba a wannan makon.Oleh Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
  continue reading
 
Send us a text Mutanen dake da sha’awar shiga harkar noma kodai don sama wa kansu abin da za su ci ko kuma don samun kudaden shiga na fuskantar kalubale. Wannan kalubale ya hada da karancin ilimin noman, da na irin shuka, da rashin gonaki da dai sauran su. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan batu tare da samar da hany…
  continue reading
 
Send us a text Tun bayan da jihar kano ta fitar da rahoton ware zunzurutun kudi har naira biliyan biyu da rabi don auratar da marasa aure a jihar ne dai batun ke ta shan suka daga bangarori daban daban a fadin Najeriya. Wasu na ganin jihar na da wasu bukatun da suka fi auratar da alumma muhimmanci da ya kamata ace gwamnatin ta mayar da hankali a ka…
  continue reading
 
A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan yanayin tattalin arzikin Kasashen duniya da hanyoyin da kan haifar da ci gaban sa da kuma karayarsa a wasu kasashen na duniya.A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan yanayin tattalin arzikin Kasashen duniya da hanyoyin da kan haifar da ci gaban sa da kuma karayarsa a wa…
  continue reading
 
Send us a text Shin shure-shure PDP take yi da ba ya hana mutuwa, ko kuwa motsi ne na alamun samun lafiya? Wannan ce tambayar da wasu ’yan Najeriya suke yi game da fito-na-fito da shugabannin jam’iyyar suka jima suna yi da juna. Tuni wasu ma suka fara diga ayar tambaya a kan makomar jam’iyyar bisa la’akari da tarin rikice-rikicen da suka dabaibaye …
  continue reading
 
Send us a text Ana ci gaba da zazzafar muhawara a shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya a kan batun samar da kotunan Shari’ar Musulunci. Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a yankin ce dai ta buƙaci hakan. Sai dai wasu ƙungiyoyi da ma ɗaiɗakun mutane a yankin suna adawa da wannan buƙata. Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lok…
  continue reading
 
Son haihuwar ‘ya’ya maza fiye da ‘ya’ya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin alummomi daban-daban. A tsakanin wasu al’ummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cika bai wa haihuwar ‘ya mace irin wannan muhimmancin ba. Ko wadanne dalilai ne suka sa wasu mutane suka fi son samu…
  continue reading
 
Send us a text Akan ce “Noma tushen arziki”. Mutane da dama za su iya bayar da labarin da ke tabbatar da hakan; domin kuwa ko ba komai idan mutum ya samu abinci ya ci ya koshi babban arziki ne. Wasu ’yan Najeriya kan shuka kayan abinci a unguwannin su don sama wa kan su abincin da za su ci. Sai dai masana na ganin da wadannan mutane za su inganta w…
  continue reading
 
Send us a text Ci gaban zamani ya zo da sauye-sauye da dama a fannonin rayuwa daban-daban ciki har da kasuwanci. A yanzu hanyar sadarwa ta zamani, ko intanet, tana taka muhimmiyar rawa wajen tallata haja ko saye da sayarwa da banarori da dama. Tuni ’yan Najeriya da dama suka yi balaguro suka koma intanet da kasuwancinsu. Shrin Najeriya a Yau na wan…
  continue reading
 
Send us a text Wadatar da al’umma da abinci abu ne mai matukar muhimmanci ga duk ƙasar dake son zama lafiya cigaba. Sai dai a Najeriya cimma wannan buri na cin karo da ƙalubale, kama daga sauyin yanayi zuwa ambaliyar ruwa, daga rashin tsaro zuwa karancin zuba jari a bangaren noma. Rahotanni sun nuna cewa adadin abincin da aka samar bai kai yadda ya…
  continue reading
 
Send us a text Kudaden crypto na cikin hanyoyin da zamani ya zo da su da nufin sauƙaƙa hada-hada a tsakanin alumma, musamman a ƙasashen da suka ci gaba. Sai dai a Najeriya, har yanzu ba kowa ne ya san wannan harka da kuma yadda ya kamata a yi ta ba, musamman duba da yadda kudin na crypto ya yi daraja a fadin duniya. Shirin Najeriya a Yau na wannan …
  continue reading
 
Samun ingattattun malamai a makarantun firamare da sakandare na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tubalin ingantaccen kuma nagartaccen ilimi a cikin al’umma. Ɗorewar wannan fafutuka ta samar da ingantaccen ilimi kuma ta dogara ne a kan samun haziƙan matasa da za su maye gurbin malaman da ake da su yanzu. Sai dai a Najeriya, alamu suna nuni da yad…
  continue reading
 
Send us a text Yanzu haka, saura mako biyu wa’adin da aka deba wa maniyyata Hajjin bana su biya kudin kujerar ya cika, amma rahotanni daga wasu sassan kasar nan na nuna cewa kalilan ne suka iya biyan. Kudin kujerar hajjin ya tsorata ’yan Najeriya a bana, bayan da hukumomi suka ce duk mai sha’awar sauke farali sai ya biya zunzuruntun kudi sama da Na…
  continue reading
 
Send us a text Ƙiyasi ya nuna cewa an yi asarar miliyoyin Naira bayan da shaguna makare da kayayyaki da motocin hawa da na haya suka ƙone ƙurmus, uwa uba kuma rayuka aƙalla 80 suka salwanta sakamakon fashewar tankar mai a Marabar Dikko da ke kusa Suleja a Jihar Neja. Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da faɗuwar tanka ta haddasa asarar dukiya da…
  continue reading
 
Send us a text A kwanakin baya farashin tumatir yayi tashin gwauron zabo a kasuwani, bayan watanni kadan kuma albasa ta tsefe kai. Ana cikin jimamin tashin farashin albasar ne sai ga na itta ya zabura. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan abubuwan da suka sa farashin citta ya yi tashin gwauron zabo a kasuwanni.…
  continue reading
 
Send us a text Rashin tsaro na ci gaba da addabar ’yan Najeriya a matakai daban-daban, a sassan kasar nan daban-daban. Yayin da a wasu yankuna ake fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya, a Abuja ana fama ne da masu kwacen motoci, da ’yan damfara, da sauran su. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wurare…
  continue reading
 
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko 'ya riƙo. A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu. Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauƙaƙa danƙon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu. Shirin Daga Laraba na wannan…
  continue reading
 
Send us a text Saye ko sayar da guraben aiki wani abu ne da yake karuwa kuma yake barazana ga ci-gaban al’umma a Najeriya. Akan yi zargin cewa mutane suna bin wasu hanyoyin da ba su dace ba kafin a ba su aiki a gwamnati. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wadannan hanyoyi da illar da suke haifar wa al’umma da kuma dabarun k…
  continue reading
 
Send us a text Bayanai na kara bayyana game da wani hari da Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kai a kan wasu kauyuka biyu na Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, wanda ya yi sanadin mutuwar farar hula akalla 15. Wadanda suka shaida faruwar lamarin dai sun ce sojojin sun kai hari da jirgi mai saukar ungulu ne a kauyukan biyu wadanda ’yan…
  continue reading
 
Send us a text A wannan zamani, ’yan Najeriya da dama ba sa samun wadataccen abinci a yini. Magidanta da dama, musamman, sun tsallake sun bar iyalansu sun shiga bariki don neman na sanyawa a bakin salati. Mene ne dalilin hakan, kuma yaya za a yi a kauce wa fadawa cikin irin wannan yanayi? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan …
  continue reading
 
A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaka da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauran su. Sai dai yayin da a da sunayen da Hausawa kan sanya wa ’ya’yansu na Annabawa ko Sahabbai ko mashahuran malaman Muslunci ne, a baya-bayan nan wasu iyaye kan aro wasu kalmomi su rika kiran ’ya’yansu da su. Mene n…
  continue reading
 
Send us a text Malamai na dauri sun karantar da cewa idan mutum ya bar karatu na kwana daya, karatun zai bar shi tsawon mako guda; idan ya bar karatu mako guda, karatun zai bar shi wata guda. Sai dai a yau, a duk lokacin da aka ce an koma makaranta bayan hutu, a kan samu rashin komawar dalibai a ranar da aka koma – a wasu lokutan ma, har da malamai…
  continue reading
 
Send us a text A duk lokacin da aka ce an biya albashi, yanayi kan sauya ga masu karba har da masu sana’oi a kasuwanni da kananan shaguna a unguwanni. Sai dai watan Janairun ko wace shekara kan zo da kalubale kasancewar an biya masu aikin albashi da wuri a cikin watan Disamba, sun kuma karar da shi a kan bukukuwan da watan kanzo dasu. Shirin Najeri…
  continue reading
 
Send us a text Ga mai son yin nazari a kan makomar bangaren ilimi a Najeriya a 2025, tanade-tanaden Kasasfin Kudi na bana ka iya zama manuniya. A kasafin kudin Gwamnatin Tarayya na 2025 dai, an ware wa bangaren ilimi sama da naira tiriliyon uku. Wannan ne kuma karo na farko da bangaren ya samu irin wannan gata. Sai dai da alamu hakan bai yi wa mala…
  continue reading
 
Send us a text A cikin ‘yan shekarun nan, matsalar tsaro ta kasance babbar kalubale a Arewacin Najeriya. Musamman a jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina da kuma jihar Sakkwato. Daga matsalar ‘yan fashi zuwa ta’addanci, yankin ya fuskanci barazanar tsaro daban daban. Duk da irin wadannan kalubale, mutanen wadannan yankuna sun nemo wasu hanyoyi daban-dab…
  continue reading
 
A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa. Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai hannu da shuni ya fito takan tubure ta ki shi. Sai dai a wannan zamani mata da dama kan fito fili suna bayyana irin saurayin da suke so, a galibin lokuta m…
  continue reading
 
Send us a text Zabukan Kananan hukumomi na cikin al’amuran da suka dauki hankali a fagen siyasar Najeriya a shekarar 2024. Duk da an gudanar da zabukan cike gurbi a wasu daga cikin jihohin Najeriya, zabukan kananan hukumomi na cikin batutuwan da ’yan Najeriya suka fi zantawa a kai, mai yiwuwa saboda ganin da ake yi cewa wadannan zabukan sun fi shaf…
  continue reading
 
Send us a text Tun bayan rantsar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a watan Mayun bara ne dai ’yan Najeriya suke ta kokawa da matsin tattalin arziki sakamakon wasu tsare-tsare da manufofi da Gwamnatin Tarayya ta bijiro da su. Wadannan manufofi sun hada da janye tallafin man fetur da kyale kasuwa ta yi halinta a kan darajar Naira da janye tallafin w…
  continue reading
 
Send us a text A baya bayan nan ana cigaba da samun hare hare da sojoji ke kaiwa kan fararen hula kamar yadda wasu suka bayyana. Ko A shekarar da ta gabata, rundunar sojin kasar nan ta kai wani hari garin Tudun biri dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna inda harin yayi sanadiyyar mutuwar gomman mutane. Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zaiyi…
  continue reading
 
Send us a text Ranar 26 ga watan disambar duk shekara ne ake rabon kyaututtuka a cigaba da gudanar da bukuwan kirsimeti wanda ake ma wannan rana da boxing day. Alumma da dama da sunji boxing day abun dake fara zuwa musu a rai shine wasan dambe da ake yi a wasu kasashe da ake kira da boxing. Shirin Najeriya A Yau zai yi duba ne kan wannan rana na Bo…
  continue reading
 
A dukkan kwanakin karshen watan Disambar kowace shekara, lokacin ne da farin ciki ke cika a fuskokin Mabiya Yesu Almasihu don gudanar da bukuwaN ranar tunawa da haihuwar sa wato kirsimeti. Sai dai, wasu darikun addinin kirista da suka hada seventh day Adventist, Jehovah Witness da ma kuma darikar Deeper Life basu yadda da gudanar da wannan biki na …
  continue reading
 
Send us a text Lokacin bukukuwa lokaci ne da ake samun karuwar zirga-zirga da hada-hadar jama’a. Wannan ne ya sa hukumomin da nauyin samar da tsaro ya rataya a wuyansu suke kara kaimi wajen ganin sun tabbatar da doka da oda. Sai dai wasu ’yan Najeriya sukan yi zargin cewa ’yan sanda kan yi amfani da wannan dama don kamen mutane babu gaira babu dali…
  continue reading
 
Send us a text Lokacin da Victoria Faith, wata baiwar Allah mai shekara 27 da haihuwa, ta je coci a Gundumar Maitama da ke birnin Abuja, cike take da kyakkyawan fatan samo abincin da za ta yi bikin Kirsimeti da shi. Amma a maimakon haka da kyar ta tsira da ranta, ta yi “sa’a” da ta farka a gadon asibiti, bayan da aka tattake ta a turmutsutsun da ya…
  continue reading
 
Send us a text A shekarun baya, idan mutum ya shiga tashoshin mota a biranen Najeriya a irin wannan lokaci, zai same su cike da jama’a da hayaniya. Sai dai a bana, a tashoshi da dama, wasu direbobin a kwance suke yayin da fasinjoji suke zaune tsawon sa’o’i suna jiran tsammanin motoci su cika. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne …
  continue reading
 
Tururuwar da mutane suke yi zuwa manyan biranen Najeriya na barazana ga wadannan alƙaryu ta fuskar tsaftar muhalli. Misali, wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa a duk sa'a daya birnin Legas kan yi baƙi 77 – hakan kuma kan haddasa karuwar sharar da ake zubarwa. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan yadda shara ke adda…
  continue reading
 
Send us a text Yayin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yake gabatar da Kudurin Kasafin Kudi na 2025, shi kuwa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio dauke hankalin jama’a ya yi da sanar da tsawaita wa’adin Kasafi na bana zuwa tsakiyar badi. Sai dai masana sun yi gargadin cewa wannan lamari ka iya haifar da rikita-rikita a bangaren tattalin ar…
  continue reading
 
Send us a text Wani rahoto da Kungiyar Likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta fitar ya nuna cewa Arewa maso Yamma ta fi kowacce shiyya yawan karuwar yara masu tamowa. A shiyyar kuma, inji rahoton, Katsina ta fi ko wacce jiha yawan masu fama da cutar. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi bincike ne don gano yadda lamarin yake.…
  continue reading
 
Loading …

Panduan Rujukan Pantas

Podcast Teratas
Dengar rancangan ini semasa anda meneroka
Main