Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya?
Manage episode 466065598 series 3311743
Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin.
Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba har da mazan ma na kauracewa wannan karatun.
Zainab Kwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai duba ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya.
771 episod