Matakan Samun Abinci A Kan Farashi Mai Rahusa A Najeriya
Manage episode 462972397 series 3311743
Wadatar da al’umma da abinci abu ne mai matukar muhimmanci ga duk ƙasar dake son zama lafiya cigaba.
Sai dai a Najeriya cimma wannan buri na cin karo da ƙalubale, kama daga sauyin yanayi zuwa ambaliyar ruwa, daga rashin tsaro zuwa karancin zuba jari a bangaren noma.
Rahotanni sun nuna cewa adadin abincin da aka samar bai kai yadda ya kamata a ce an samu ba ta dalilin wadannan matsaloli.
Ko me ya kamata a yi don shawo kan wannan mi’ara koma baya da harkar samar da abinci take yi a Najeriya?
Wannan shi ne batun da aka duba yayain Taron Muhawara na Shekara-Shekara na Daily Trust nab ana, kuma a kansa shirin Najeriya a Yau za iyi tsokaci.
773 episod