Kalubalen Dake Neman Durkushe Kafafen Rediyo A Arewa
Manage episode 466448795 series 3311743
Rediyo na daga cikin kafofin da alumma da dama suka dogara dasu don jin labarai, shirye shirye da kuma nishadi.
Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa da alumma dama kai musamman duba da yadda aka bada shaidar cewa tafi kowace kafar media saurin yada bayanai ba a cikin birane ba, har ma da yankunan karkara.
Sai dai a wannan gaba ana ganin rediyo a Arewacin kasar nan na samun koma baya la’akari da yadda a wasu lokutan wasu gidajen rediyon ke kanannadewa su bace ba tare da jin duriyar su ba.
769 episod