Anya Jam’iyyar PDP Za Ta Kai Labari A Fagen Siyasar Najeriya Kuwa?
Manage episode 464181479 series 3311743
Shin shure-shure PDP take yi da ba ya hana mutuwa, ko kuwa motsi ne na alamun samun lafiya?
Wannan ce tambayar da wasu ’yan Najeriya suke yi game da fito-na-fito da shugabannin jam’iyyar suka jima suna yi da juna.
Tuni wasu ma suka fara diga ayar tambaya a kan makomar jam’iyyar bisa la’akari da tarin rikice-rikicen da suka dabaibaye ta.
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai nazari don bankado abin da yake faruwa da jam’iyyar yayin da 2027 take kara matsowa.
769 episod