Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Sanya Wasu ‘Yan Najeriya Ajiye Ababen Hawan Su?
Manage episode 447244108 series 3311743
Tsadar man fetur a Najeriya ya tilastawa da yawa daga cikin ‘yan kasa ajiye ababen hawan su inda suka koma bin na haya don zuwa wuraren aiki, Ziyara da sauran zirga-zirgar su ta yau da kullum.
A baya manyan biranen Najeriya su kan cika su batse da ababen hawa da kan yi zirga-zirga da kai kawo, wanda wasu suke ganin wadata da fin karfin bukatun yau da kullum ne ke sanya hakan.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana yayi duba ne kan yanda wasu ‘yan Najeriya suke ajiye ababen hawan su suna komawa bin na haya....
690 episod