Ina Aka Kwana A Binciken Harin Tudun Biri?
Manage episode 393306379 series 3311741
Yanzu wata guda kenan tun bayan da sojoji suka yi kuskuren kai hari kan masu Maulidi a garin Tudun Biri dake jihar Kaduna.
Harin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 100, inda hukumomi da gwamnati ba su yi wata-wata ba wajen daukar alhakin hakan da kuma bayyana cewa za a yi abin da ya dace wajen bin hakkin waɗanda lamarin ya shafa.
Toh shin zuwa yanzu wane hali ake ciki? Ko an fara bincike kuwa? Ina kudaden da aka tara na tallafi suke?
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nazari na musamman a kan matakin da ake kai na bincike kan harin.
191 episod