APCS awam
[search 0]
lebih
Download the App!
show episodes
 
Artwork

1
Najeriya a Yau

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

icon
Unsubscribe
icon
icon
Unsubscribe
icon
Mingguan+
 
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
  continue reading
 
Loading …
show series
 
Send us a text A siyasar Najeriya, akwai ka’idoji da dokoki da ke tsara yadda ake gudanar da zaɓe, ciki har da lokacin da doka ta amince a fara yaƙin neman zaɓe. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, wato INEC, ita ce ke da alhakin bayyana jadawalin zaɓe da kuma ranar da ‘yan takara za su fara neman goyon bayan al’umma a hukumance. Sai dai duk da waɗannan tanade-t…
  continue reading
 
Send us a text A cikin ‘yan kwanakin nan, siyasar Najeriya ta sake daukar sabon salo, bayan barkewar takaddama tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, da manyan shugabannin jam’iyyar (APC). Jam’iyyar APC na kallon yadda Wike — wanda ba cikakken ɗan jam’iyyar ba ne amma ke rike da mukami a karkashin gwamnatinta — ke yin katsaland…
  continue reading
 
Send us a text Harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai kasuwar Daji da ke karamar hukumar Borgu a Jihar Neja ya sake jawo hankalin al’umma kan matsalar rashin tsaro da ke kara ta’azzara a yankunan karkara na Arewa ta Tsakiya. Kasuwar Daji, wadda ke zama cibiyar hada-hadar kasuwanci ga manoma, ‘yan kasuwa da mazauna kauyuka makwabta, ta kasance wuri na …
  continue reading
 
Send us a text A fagen siyasar Najeriya a halin yanzu, ana ta ce-ce-ku-ce kan wacce ce babbar jam’iyyar adawa da za ta iya tsayawa ƙafada da ƙafada da jam’iyyar APC mai mulki. Wannan takaddama ta fi karkata ne tsakanin jam’iyyar PDP, wacce ta dade tana taka rawa a matsayin babbar jam’iyyar adawa bayan ficewarta daga mulki a 2015, da kuma jam’iyyar …
  continue reading
 
Send us a text Shekarar 2026 ta zo a wani lokaci da ’yan Najeriya da dama ke fuskantar matsin tattalin arziki, da sauye-sauyen siyasa, da kuma ƙalubalen rayuwa da ke bukatar sabon tunani. Wannan ba lokaci ba ne na fatan samun sa’a kawai, lokaci ne na tsara hanya, da ɗaukar matakai, da yin gyara a rayuwar yau da kullum. A wannan shiri, za mu duba ya…
  continue reading
 
Send us a text Yayin da muke bankwana da shekarar 2025, siyasar Najeriya ta kasance cike da sauye-sauye, rikice-rikice, da kuma manyan al’amura da suka shafi iko, jam’iyyu da shugabanci. Shekarar ta shaida sauyin sheƙa na ‘yan siyasa, rikicin cikin gida a wasu jam’iyyu, da kuma fafutukar karɓar ragamar mulki a jihohi da matakin tarayya, lamarin da …
  continue reading
 
Send us a text A shekarar 2025, Najeriya ta fuskanci manyan ƙalubalen tsaro da suka fi daukar hankali, musamman hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, da ta’addanci a jihohin Arewa kamar Zamfara, da Katsina da Sokoto da Kaduna da kuma Borno. Hare-haren sun yi sanadin rasa rayuka, da rufe makarantu, da kaura daga gidaje, da kuma durkushewar har…
  continue reading
 
Send us a text A duk faɗin Arewacin Najeriya, ana gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna, duk da kasancewar Musulmai ne suka fi rinjaye a yawancin yankuna. Kiristoci kan yi bukukuwansu cikin mutunta al’adar Musulmai, yayin da Musulmai kuma ke nuna goyon baya ta hanyar gaisuwa, da tsaro, da mu’amala ta zamantakewa. A…
  continue reading
 
Send us a text A yayin da al’ummar Kirista a sassa daban-daban na ƙasar nan ke gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin walwala, da annashuwa da haɗuwa da iyalai, akwai kuma waɗanda wannan lokaci ya zo musu cikin ƙunci da jimami. Waɗannan su ne mutanen da matsalolin tsaro—kamar hare-hare da rikice-rikice—suka tilasta musu barin gidajensu da muhallansu.…
  continue reading
 
Send us a text Gabannin bukukuwan Kirsimeti, kasuwanni a sassan ƙasar nan sun cika sun bunkasa. Jama’a na ci gaba da zirga-zirga domin sayen kayan bukukuwa, yayin da ‘yan kasuwa ke kokarin jawo hankalin masu saye ta hanyar daidaita farashi. A wannan shekarar, alamu sun nuna ba a samu hauhawar farashin kayayyaki a yawancin kasuwanni ba, sai dai wasu…
  continue reading
 
Send us a text Takaddama mai zafi ta dabaibaye sabbin dokokin haraji da Majalisar Tarayya ta amince da su, bayan zarge-zargen cewa an samu sauye-sauye a cikin dokokin bayan an kammala dukkan matakan amincewa da su a majalisa. Batun da ya taso ya jawo cece-kuce daga ‘yan majalisa, jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula, inda suke tambayar sahiha…
  continue reading
 
Send us a text Gobara a irin wannan yanayi na iska musamman a kasuwanni da gidaje ba sabon abu bane kuma ba abun mamaki ba. Wasu kafintoci dake aiki a kasuwar lale dake unguwar Tal’udu a karamar hukumar Gwale dake jihar Kano sun wayi gari da alhinin gobarar da ta yi sanadiyyar raba su da hanyar abincinsu. Wannan gobara da ba’a san musabbabinta ba t…
  continue reading
 
Send us a text Murabus din da Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai ta kasa Ahmed Farukh ya yi daga mukaminsa ya sa ‘yan Najeriya da dama na ta tofa albarkacin bakinsu musamman a bangaren harkokin mai. Murabus din na zuwa ne bayan doguwar takaddama tsakaninsa da Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote kan batutuwa da dama. Shin ko w…
  continue reading
 
Send us a text Takunkumin da Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanya wa wasu ‘yan Najeriya ya sake jawo hankali kan irin tasirin manufofin ƙasashen waje ga rayuwar mutane da tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya. Wannan takunkumi, wanda ya haɗa da hana shiga Amurka, da toshe kadarori ko hana mu’amala da wasu hukumomi da kamfanonin Amurka, ba wai hu…
  continue reading
 
Send us a text Batun matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na mayar da shalkwatar Bankin Masana’antu zuwa jihar Legas ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya. Wannan mataki ya tayar da mabanbantan ra’ayoyi daga bangarori daban-daban na al’umma, inda wasu ke kallonsa a matsayin shawara mai ma’ana da za ta karfafa harkokin masana’antu da ja…
  continue reading
 
Send us a text A ’yan shekarun nan, lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara—wanda a da ake ɗauka a matsayin lokacin farin ciki, da haɗuwa da iyalai, da tafiye-tafiye—ya fara sauya salo ga mutane da dama. Maimakon shirye-shiryen ziyartar ’yan uwa ko halartar bukukuwa a garuruwa daban-daban, mutane da yawa yanzu suna cike da fargaba da damuwa. Babban dal…
  continue reading
 
Send us a text A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen lokaci don isar da darussa tare da kwarewa…
  continue reading
 
Send us a text A yau al’ummar mu na fuskantar barazana ta wata siga da ba kasafai ake gane ta ba, wato guba da ke shiga jikin ɗan Adam ta hanyar abinci irin su nama, kifi, madara da sauran kayayyakin da muke ci a kullum. Sau da yawa dabbobi ko kifaye suna cin wasu tsirrai, ganye, ko ababen da ke dauke da sinadarai masu haɗari, waɗanda daga baya suk…
  continue reading
 
Send us a text Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan. Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na buƙatar abubuwa masu yawa kafin su iya ɗaukar wannan nauy…
  continue reading
 
Send us a text Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka su a cell? ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fash…
  continue reading
 
Send us a text Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya. An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin mata a duniya ke fama da wannan cuta. Abin damuwa shi ne cewa yawancin lokuta ana gano cutar ne a kurarren lokaci, …
  continue reading
 
Send us a text A mafi yawan ƙasashen duniya, ana ɗaukar jakadu a matsayin fuskar ƙasa kuma ginshiƙan hulɗar diflomasiyya. Saboda haka, akwai muhimman halaye da suke tilas jakadan ƙwarai ya mallaka domin ya wakilci ƙasarsa cikin mutunci, da nagarta da kwarewa. Tun bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sunayen jakadu da yake sa ran maj…
  continue reading
 
Send us a text Sheikh Dahiru Usman Bauchi, fitaccen malamin addinin Musulunci, masanin tafsiri, kuma jagoran darikar Tijjaniyya, shahararre ne saboda iliminsa mai zurfi da tasirin da ya yi a fagen addini da tarbiyya a Najeriya da ma ƙasashen Yammacin Afirka. Sheikh Dahiru Bauci ya shafe sama da shekaru saba’in yana koyar da ilimi, ya gudanar da tar…
  continue reading
 
Send us a text A cikin shekarun nan, matsalolin tsaro a Najeriya kamar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ’yan bindiga suna kara ta’azzara, lamarin da ya sanya al’umma da masana tsaro ke tambayar wace hanya ta fi dacewa gwamatani ta yi amfani da shi wajen kawo karshen wadannan matsaloli da suka ki ci su…
  continue reading
 
Send us a text Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita. Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da …
  continue reading
 
Send us a text A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative. Manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa dalibai suna iya zuwa ma…
  continue reading
 
Send us a text Hukuncin da kotun tarayya ta Abuja ta yanke wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ya sake tayar da kura a tsakanin magoya bayansa, ‘yan yankin Kudu maso Gabas, da al’ummar Najeriya gaba ɗaya. Yayin da gwamnati ke cewa hukuncin ya biyo bayan dogon shari’a da hujjoji da suka tabbatar da aikata laifukan da ake tuhum…
  continue reading
 
Send us a text Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ci…
  continue reading
 
Send us a text Matsayar doka ta zama babbar abun tattaunawa a Najeriya yayin da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron ta na kasa duk da mabanbantan hukunce hukunce daga kotuna biyu. Umarnin kotu guda yana goyon bayan taron, ɗayan kuwa ya haramta shi gaba ɗaya. Wadannan hukunce hukunce ba baiwa jam’iyyar damar yi ko haramta musu taron kadai suka yi ba, …
  continue reading
 
Send us a text A duk shekara bayan girbin damina, ana sa ran manoma su ci gaba da noma a lokacin rani domin tabbatar da wadatar abinci da bunkasar tattalin arziki. Sai dai hakan na fuskantar kalubale da dama da ke hana yawancin manoma shiga noman rani. Kamar yadda masana suka sha bayyanawa, akwai dalilai da dama dake hana manoma shiga noman rani a …
  continue reading
 
Send us a text A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar. Kazalik…
  continue reading
 
Send us a text A yayin da tattaunawa kan makomar ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ke ci gaba da ɗaukar hankali, batun yadda za a haɗa jami’o’i masu zaman kansu cikin tsarin ƙungiyar ya sake tasowa. Wasu na ganin wannan sabon yunƙuri zai iya zama sabuwar hanyar ƙarfafa hadin kai tsakanin malamai, yayin da wasu ke gargadin cewa hakan na i…
  continue reading
 
Send us a text Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma. Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.…
  continue reading
 
Send us a text Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta. A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta. Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suk…
  continue reading
 
Send us a text Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi. Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika b…
  continue reading
 
Send us a text Ana ta ce-ce- ku-ce kan batun da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na kawo dakarun kasar sa Najeriya don taimakawa wajen yaki da matslar tsaro. Yayin da wasu ke ganin hakan abun san barka ne, wasu kuwa tofin Ala tsine suka yi ga wannan batu. Shin ko me zai faru idan aka kawo dakarun kasar Amurka Najeriya don shawo matsalar tsa…
  continue reading
 
Send us a text Duk da cewa gwamnati na da dubban kwararrun malamai a makarantunta, har yanzu ana ganin ɗaliban makarantun gwamnati na kasa da na makarantun masu zaman kansu wajen ƙoƙari da kuma sakamakon jarabawa. Wannan matsala ta daɗe tana jawo muhawara tsakanin iyaye, malamai da hukumomin ilimi. Wasu na ganin matsaloli ne da ba za su rasa nasaba…
  continue reading
 
Send us a text Tun bayan sauya hafsoshin tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ne dai mutane da dama keta tofa albarkacin bakinsu, yayin da wasu ke ganin hakan zai taimaka wajen yaki da rashin tsaro, wasu kuwa na ganin duk jama’ar ja ce. Shin ko sauya hafsoshin tsaro zai kawo karshen fargaban da al’umma ke yi? Wannan shine batun da shirin …
  continue reading
 
Send us a text A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an sake ganin karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP musamman a yankin Arewa maso Gabas. Kazalika, ko a kwanan nan ma anga irin wadannan hare hare. Wadannan hare-haren sun fi karkata kan sansanonin sojoji, inda ake samun asarar rayuka da dama, da kuma lalata kayan aikin gwamnati. Rahotanni daga B…
  continue reading
 
Send us a text A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden shiga da kuma rage dogaro da albarkatun mai. Sai dai, jama’a da dama ba …
  continue reading
 
Send us a text Cutar Cerebral Palsy, wadda ake kira Ciwon tsukewar kwakwalwa, na daga cikin manyan matsalolin lafiyar yara da ke tasowa tun daga haihuwa. Wannan cuta tana faruwa ne sakamakon rauni ko lalacewar wani ɓangare na kwakwalwa da ke kula da motsi, magana, da daidaiton jiki. A mafi yawan lokuta, cutar tana bayyana ne tun daga ƙuruciya, a wa…
  continue reading
 
Send us a text Tun bayan fara shari’ar Nnamdi Kanu a shekarar 2021 mutane da dama suke bayyana ra’ayoyinsu a kan sake shi ko a kyale shari’a ta yi halinta. Hasali ma har zanga-zanga wasu ‘yan Najeriya suka kira don bayyana bukatar sakin shugaban na ‘yan aware. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan ko ya dace a saki Nnamdi Ka…
  continue reading
 
Send us a text Cire darasin Lissafi daga jerin wajibcin da ake buƙata domin samun shiga manyan makarantu ya samu karɓuwa daga wasu ɓangarori na dalibai da malamai. Wasu dalibai sun nuna farin ciki da wannan mataki, suna ganin zai sauƙaƙa musu damar samun shiga jami’a da sauran manyan makarantu ba tare da shan wahalar lissafi ba. Sai dai wasu masana…
  continue reading
 
Send us a text Shekara da shekaru kungiyar malaman jami’oi ASUU ta kwashe ta na gudanar da yajin aiki ba tare da samun biyan bukata ba. Irin wannan yajin aiki da kungiyar malaman ke shiga ya jefa dalibai da malaman da ma harkar ilimi cikin halin ni ‘yasu a Najeriya. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wasu hanyoyin da kungiy…
  continue reading
 
Send us a text A duk lokacin da a ka samu canjin shugabanci, hakan kan zo da kalubale da dama. Muƙamin shugabancin Hukumar Zabe ta kasa na daga cikin mukamai a Najeriya da 'yan kasa ke cece-kuce a kai. Ko wadanne irin Kalubale ne ke gaban sabon shugaban hukumar zabe ta kasa? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari…
  continue reading
 
Send us a text A tsarin mulkin Najeriya, an bai wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tare da sauran mambobinta. Wannan iko yana daga cikin muhimman nauyukan da ke hannun shugaban ƙasa domin tabbatar da cewa ana gudanar da zaɓe cikin tsari, gaskiya da adalci. Sai dai, kafin wanda shugaban ƙasa ya naɗa ya fa…
  continue reading
 
Send us a text Halin matsin tattalin arziki ya tilasta da yawa daga cikin mutane zama a bacoci a garin Abuja da wasu biranen Najeriya. Mutane a birane kamar Abuja da Legas Da Fatakwal na cikin halin matsi sakamakon rashin ingattaccen muhalli. Ko wannen irin rayuwa irin wadannan mutanen ke yi? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lo…
  continue reading
 
Send us a text A zamanin yau na fasahar zamani, musamman fasahar kirkirarriyar basir ta (AI), harkokin sana’o’i da dama suna fuskantar sauye-sauye masu girma. Daya daga cikin sana’o’in da ke cikin babban hadari shi ne sana’ar ɗaukar hoto musamman irin wadanda ke kashe makudan kudi wajen sayen kyamara da bude katafaren gidajen daukar hoto. A da, mut…
  continue reading
 
Send us a text Batun siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Wannan batu ya tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masana, da ‘yan siyasa da ma al’umma. Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon shugaban ƙasan, har …
  continue reading
 
Loading …

Panduan Rujukan Pantas

Podcast Teratas
Dengar rancangan ini semasa anda meneroka
Main