2023: Yadda Tinubu Ya Karbi Batun Takarar Osibanjo
Manage episode 325285268 series 3311743
Hankalin ’yan Najeriya ya koma kan yadda Uban Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ke neman takarar shugaban kasa ya ji da fitowar Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osibanjo, takarar kujerar.
Da wace fuska Tinubun ya karbi aniyar ta Osibanjo, wanda ake kallo a matsayin yaron gidansa? Shin wuyan Osinbajo ya kai yanka? Wadanne kalubale takarar tasa take tattare da su? Sannan tsakanin shi da Tinubu wa zai dagula wa wani lissafi?
Shirin Najeriya A Yau na wannan na tafe gamsassun bayanai.
549 episod