Asalin ta’addanci a Zamfara
Manage episode 324106083 series 3311741
Jihar Zamfara ta yi suna a duniya a shekarar 2000, sanadiyyar kaddamar da shari’ar Musulunci.
Jama’a sunyi ta zancen Jihar da sa albarka, suna kuma kallon ta a matsayin wani wuri da za a samu wanzuwar adalci saboda abinda ake sa ran wannan sabon tsarin mulkin zai tabbatar.
Sai dai a baya-bayanan, Jihar ta tsinci kanta a bakin jama’a a wannan karon ana tir da abinda ke fitowa na ta’addanci da duk wani irin rashin mutunci da mai tunani zai tunano.
Daga ina wannan matsala ta samo asali?
Su wa ake zargi da shuka wannan bala’i da ya addabi yankin Arewa baki daya?
152 episod