Muslim Muhammad Yusuf awam
[search 0]
lebih
Download the App!
show episodes
 
Artwork

1
Najeriya a Yau

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

icon
Unsubscribe
icon
Unsubscribe
Mingguan+
 
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
  continue reading
 
Artwork

1
Daga Laraba

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

icon
Unsubscribe
icon
Unsubscribe
Mingguan
 
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
  continue reading
 
Loading …
show series
 
Send us a text Zazzabin cizon sauro, wato malaria, na cikin cututtuka mafiya shahara da kuma hadari a Najeriya. Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa Najeriya na da kaso mafi girma na mace-macen da cutar take haifarwa a duniya. Sau da yawa wanda ya kamu da cutar ta malaria kan sake kamuwa da ita bayan ya warke. Ko me ya sa magung…
  continue reading
 
Send us a text Tun zamanin kaka da kakanni ake gudanar da kananan sana’oi, wanda alumma ke dogaro dasu don biyan bukatun su na yau da kullum. Irin wadannan sana’oi sun hada da saka, jima, balangu, suyan kosai ko masa da dai sauran sana’oi da alumma keyi. A da can baya irin masu wadannan sana’a sun dogara ne da masu wucewa a bakin hanya don siyar da…
  continue reading
 
Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika daya. Masu kananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durkushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta. Shirin Daga Laraba na wannan …
  continue reading
 
Send us a text Ko kun san tanadin da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya yi game da Ofishin Mataimakin Shuaban Kasa da ayyukansa da alhakin da ya rataya a wuyansa? Kundin na Tsarin Mulkin Kasa ne dai kundin dokoki mafi karfi a Najeriya wanda ya kunshi tanade-tanade a kan dukkan al’amuran da suka shafi alhakin da ya rataya a wuyan shuggabanni da ma al’umma…
  continue reading
 
Send us a text A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga ɗimbin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu matsalolin na ƙara Kunno Kai. Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar kalubale iri-iri kama daga hare-haren da ake zargin na kungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas, zuwa ga sabbin kashe-kashe a wasu garuruwan jihoh…
  continue reading
 
Send us a text Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. Mai yiwuwa hakan ne ya sa matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka shiga ofishin ’yan sanda, su kuma fita ba tare da wani ya harare su ba, balle ya kama su. ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen …
  continue reading
 
Send us a text Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi …
  continue reading
 
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko ‘ya riƙo. A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu. Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauƙaƙa danƙon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu. Shirin Daga Laraba na wannan…
  continue reading
 
Send us a text A yanzu haka, al’ummar jihar Filato na cikin fargaba da tashin hankali sakamakon jerin hare-haren da suka afku a wasu sassan jihar, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, wasu kuma suka tsere daga muhallansu. Ko mene ne dalilin sake fitowar rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin da ake ganin an fara samun zaman lafiya? Shirin Na…
  continue reading
 
Send us a text A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zulumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin kungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar. Wadannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da ikirarin Gwamnati na cewa an yi nasarar nakasa kungiyar. Ko mene ne dalilin sake farfadowar kungiyar ta Boko Haram a wannan lokaci? Wanna…
  continue reading
 
Send us a text A Najeriya ana tafka muhawara a kan yadda farashin danyen man fetur yake kara faduwa a kasuwannin duniya. Wannan lamari dai ya haddasa damuwa a zukatan wasu ’yan Najeriya, kama daga masana tattalin arziki zuwa ga jami’an gwamnati, kasancewar danyen mai ne mafi muhimmanci a cikin hanyoyin samun kudin shiga. Sai dai tambayar da wasu ’y…
  continue reading
 
Send us a text Irin dangantakar dake kasancewa tsakanin abokai na da matukar tasiri ga farin cikin wadannan abokai, ta yadda a wasu lokutan ma baka iya banbancewa tsakanin ‘yan uwan su na jini da kuma abokai. Irin wannan dangantaka ya kamata ne ace ana samun shi a wurin wadanda suke uwa daya uba daya ko kuma wadanda suke uba daya. Sai dai a yayin d…
  continue reading
 
Tun kaka da kakanni an san Hausawa da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su. Mai yiwuwa wadannan dabi’u ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka. To amma a zamanin yau ba abin mamaki ba ne a samu matar aure ta kalli kwayar idon mijinta, ta kuma kira shi da sunansa na yanka. A kan wannan…
  continue reading
 
Send us a text A zamanin yau, ba kira da tura saƙo kawai ake yi da wayar hannu ba; baya ga haka, muhimmiyar hanya ce ta samun kuɗi da bunƙasa sana’o’i. Ko kun san dabarun amfani da wayoyinku don samun kuɗaɗen shiga? Idan ba ku sani ba, ko kuma kuna buƙatar ƙarin sani, ku biyo mu a shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci.…
  continue reading
 
Send us a text Shirin bautar ƙasa wanda aka kafa tun a shekarar 1973, an kirkire shi da nufin haɗa kan matasa daga kowane lungu da saƙo na ƙasar nan, domin fahimtar juna da kawar da wariyar yanki da kabilanci. Amma a yau, bayan shekaru fiye da arba'in da biyar da fara wannan shiri, jama’a da dama na tambaya: ko har yanzu shirin na da tasirin da aka…
  continue reading
 
Send us a text Cututtuka da dama suna Kamari a Najeriya wanda a mafi yawancin lokuta ma wadanda ke dauke da irin wadannan cututtukan basu da masaniyar suna dauke da su. Kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana, zaman lafiya, rashin matsalar kwakwalwa, da samun wadata na daga cikin abubuwan dake tabbatar da lafiyar bil’adama. Wata cuta da ta a…
  continue reading
 
Send us a text Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa. Daya daga cikin manyan sauyin da ak…
  continue reading
 
Tun bayan kisan mafarauta 16 dake hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi dake karamar hukumar Esan dake jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu. A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na ‘yan kasa masu cikakken …
  continue reading
 
Send us a text Alqurani mai girma a cikin suratul Baqarah Allah ya wajabta wa musulmi da suka cika wasu sharudda azumtar watan Ramadana. Kamar yadda malamai suka sha fadi, wannan wata na dauke da wasu falala maras misaltuwa da bawa kan samu idan ya maida kai wajen ibada don samun rabauta daga ubangiji. Kazalika hadisai sun ruwaito kan falalar azumt…
  continue reading
 
Send us a text Watan azumin ramadana kan zo da sauye sauye da dama da suka hada da kara kaimi wajen bauta wa ubangiji, samun lada ta hanyar ciyar da alumma da kuma falala masu yawa da basu misaltuwa. Wani sauyi da watan azumin watan ramadana ke zuwa dashi shine canjin yanayin ciman alumma, inda mutane ke canzawa daga cin abinci sau uku ko sama da h…
  continue reading
 
Send us a text Lokutan sallah kamar yadda aka sani lokacin ne na farin ciki, nuna godiya ga ni’imar da Allah yayi mana da kuma bauta. Kazalika lokacin ne da zamu lura da tabbatar da aiyukan da zamu aikata su zama ingattattu. Ko wadanne irin abubuwa ne mutane ya kamata su aikata kafin da kuma ranar sallah? Wadanne hanyoyi za a bi don tabbatar da zam…
  continue reading
 
Send us a text Yau a Najeriya da yawa daga cikin matasa na fuskantar kalubale musamman wajen biya ma kan su bukatun su na yau da kullum sakamakon yanayin tattalin arzikin kasa, rashin aikin yi da kuma tsadar rayuwa. A wasu lokutan irin wadannan matasa sun yi karatu, wasu ma na da sana’oin su na hannu amma rashin aiki mai gwabi da zai biya musu buka…
  continue reading
 
A duk lokacin da aka ce lokutan bukukuwa sun karato, akan samu sauyi a dukkan alamura. Daya daga cikin irin wadannan sauyi da ake samu shine na farashin kayayyakin masarufi. A wasu lokuta, akan samu tashin farashin irin wadannan kayayyaki, a wasu lokutan kuma akasin haka. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai tattauna ne kan farashin kayayyakin ma…
  continue reading
 
Send us a text Mulkin demokradiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin dan adam. A lokacin da ta baka damar tsayawa don a zabe ka kan wani mukami, kazalika ta baka damar zaben wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka. Wani abun da demokradiyyar ta baiwa alumma dama a kai kuma shine na yin kiranye ga wakilan da suka zaba musamman idan wadan…
  continue reading
 
Send us a text Hausawa sunyi gaskiya da suka ce ‘yawan mutane sune kasuwa’. Yawan hada hadar da ake yi tsakanin ‘yan kasuwa da abokan cinikin su na daya daga cikin abun da zai tabbatar maka kasuwanci na gudana kamar yadda ake so. Sai dai da Zarar ance watan Ramadana ya kama wasu daga cikin kasuwanci kan samu nakasu, inda wasu kuma ke samun habbaka.…
  continue reading
 
Send us a text Shekaru da dama kenan da hukumomin duniya ke gudanar da tarurruka da dama kan zakulo hanyoyin da za a kawo karshen dumamar yanayi a duniya. Dumama ko canjin yanayi na cigaba da barazana ga duniya, inda ake samun sauye sauye ga yanayi da wasu abubuwa da masana ke bayyana ka iya kara ta’azzara in ba’ayi wani abu a kai ba. Daya daga cik…
  continue reading
 
Send us a text Sana’a na taka muhimmiyar rawa wajen habbaka tattalin arzikin alumma. Alumma da dama musamman a wannan lokacin na kara bayyana alfanun koyan sana’ar hannu don dogaro da kai maimakon dogara da aikin gwamnati ko na kamfani. Sai dai ana zargin wasu masu sana’ar hannu da rashin cika alkawari a wurin sana’ar su. Irin wadannan masu sana’ar…
  continue reading
 
A karshe dai hasashen da wasu ke yi a Ribas ya tabbata, inda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci, ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa, da ma ''yan majalisar dokokin jihar. Sai dai bayan ayyana wannan doka da shugaban kasar ya yi 'yan Najeriya da dama suna ta bayyana ra’ayoyinsu kan wannan lamari. Yayin da wasu suke …
  continue reading
 
Send us a text Mallakan Muhalli na daya daga cikin burin kowanne dan Najeriya. Sai dai wannan buri a mafi yawan lokacin baya cika musamman ga masu matsakaitan samu. Kananan ma’aikata da mafi karancin albashin su yake naira dubu saba’in ba zai ciyar dasu, ko tufatar dasu ba, ballantana har suyi tunanin mallakan muhalli nasu na kashin kansu. Sai dai …
  continue reading
 
Send us a text Duk da kukan rashin aikin yi da ako da yaushe ke cigaba da addabar ‘yan Najeriya, a wasu lokutan ba rashin aikin yi ne matsalar ba, wadanda zasu cike guraben ayyukan ne suka yi karanci a Najeriya. Alkaluma na cigaba da bayyana dubban ‘yan Najeriya ne dai ke fito wa daga manyan makarantun kasar a kowace shekara. A yayin da da yawa bas…
  continue reading
 
Send us a text Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi. Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika b…
  continue reading
 
Send us a text Masu iya magana kan ce dole uwar na ki. Matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa musamman a Arewacin Najeriya tana tilasta wa wasu al’ummomi zakulo hanyoyin samun sa’ida ko yaya suke. Daya daga cikin wadannan hanyoyi da wasu al’ummomi suka runguma ita ce kulla yarjejeniya da ’yan bindigar dake addabar yankunansu. Shin ko cimma yarjej…
  continue reading
 
Bayan dunbum falala, da yawan samuwar ibadun dake kara kusanta bayi ga ubangijin su, da azumin watan ramadana ke zuwa dashi kamar yadda malamai suka saba fada mana, Hakazalika Kuma a watan na Ramadan dai na zuwa da wata alada mai dimbin tarihi dake debe wa alumma musamman na arewacin Najeriya kewa. Wannan aladar itace ta tashe da ake fara yinta da …
  continue reading
 
Send us a text Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da daukar dumi yayin da ’yan kasa da dama suka yi kasake suna jiran girgiza ta gaba wadda wasu suke ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya diga mata dan ba. A baya-bayan nan dai an yi ta tsegunguma da rade-radi a kana bin da wasu jiga-jigan ’yan siyasar kasar nan, musamman ’yan ad…
  continue reading
 
Send us a text Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki. Sai dai a lokacin da wadannan mutane suke samun rangwame, akwai wadanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu. Sau da dama irin wadannan mutane sai sun fita sun yi aiki a…
  continue reading
 
Send us a text Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yake kara dankon zumunci da kaunar juna da albarka a tsakanin al’umma. Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu Karin kusanci da shakuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci. Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da tare da iyalin su al’ada. Shin ko m…
  continue reading
 
Send us a text Fiye da wata guda ke nan tun bayan da Matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita. Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa wato NNPCL ya sanar da rage nasa farashin. Sai dai har yanzu ba a ga ragin a gidajen mai ba. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi na…
  continue reading
 
Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale – ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza shiryawa. Wani rukunin wadannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a k…
  continue reading
 
Send us a text A aladance, a duk lokacin da aka ce watan Ramadana ya karato samari da ‘yan mata kan yi musayar kyaututtuka don kyautata wa abokan zaman su. Misali, a lokacin azumi samari kan sayi kayan bude baki da suka hada da madara, kwai, da sauran kayan makulashe wanda ake yiwa lakabi da ‘’Ramadan Basket’’ a turance don kaiwa ‘yan matan su. Sai…
  continue reading
 
Send us a text Yanayin tsadar rayuwa da ake ciki ya sa dole a yi tattalin kudin da ake kashewa. An saba da Ramadana ana yawan yin girke-girke da kayan buda baki iri-iri, amma kuma wannan azumin ya zo cikin yanayi na matsin tattalin arziki. Shirin Najeriya a Yau ya duba hanyoyin da za ku yi girke-girken da yawa yadda aka saba cikin sauki ba tare da …
  continue reading
 
Send us a text Alumma na yin azumi ne bisa dalilan addini don samun lada kamar yadda Allah ya umurta a cikin Qurani mai girma. Sai dai daga baya binciken masana kimiyya ya gano cewa bayan lada da ake samu daga yin azumi, akwai wasu alfanu da mai azumi ke samu ga lafiyar jikin shi da suka hada da inganta karfi da zurfin tunani zuwa fitar da gurbatat…
  continue reading
 
Send us a text Wutan lantarki a Najeriya ya zama ginshikin rayuwa da alumma basa iya rayuwa ba tare dashi ba. A duk lokacin da aka ce an dauke shi zaka ga yadda alumma kan shiga cikin matsanancin hali, wasu da dama sun ta’allaka ne dashi wajen tafiyar da harkokin su na yau da kullum, kai har ma da kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkw…
  continue reading
 
A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A al’adance, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son …
  continue reading
 
Send us a text Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa? Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl? Yayin da ake shirye-shiryen tarbar watan Ramadana, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nau’ukan dabino da alfanunsa ga dan’Adam, musamman mai azumi.Oleh Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
  continue reading
 
Send us a text Cutar kyandar biri da aka fi sani da Mpox ta kara bulla a Najeriya. Na baya bayan nan shine wanda ta bulla a jihar Filato inda aka samu wadanda suka kamu da ita mutum 11 da sai wanda ya rasa ransa mutum daya. Cutar ta kyandar biri ta bulla ne a kananan hukumomi biyar da suka hada da Jos ta Arewa, Bokkos, Shendam, Mangu da kuma Kenke.…
  continue reading
 
Send us a text A daidai lokacin da wasu alumma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci a kasuwanni kamar su shinkafa, masara da sauran kayan hatsi. Shima farashin flawa da ake amfani dashi wajen sarrafa biredi, gurasa da sauran makulashe ya sauka a kasuwa. Sai dai duk da saukar da farashin flawar tayi, alumma na cigaba da kokawa kan yadda har y…
  continue reading
 
Send us a text Tun bayan bayyana kafa Gwamnatin Bibiya ko kuma Shadow government a turance da wata kungiya karkashin jamiyyar APC a jihar kano tace zata yi ne ne dai alumma da dama keta jefa ayar tambaya kan halascin wannan gwamnati. Kungiyar dai ta bayyana cewa zata kafa wannan gwamnati ne don bibiyan ayyukan gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf don …
  continue reading
 
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan …
  continue reading
 
Send us a text A kwanakin baya ne dai shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kirkiri sabbin hukumomin shiyyoyin kasar nan da nufin kawo cigaba ga wadannan shiyyoyi. Gabanin kirkirar wadannan hukumomin, gwamnatin da ta gabata karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ce ta fara kirkirar hukumar raya yankin Neja Delta bayan wasu kalubal…
  continue reading
 
Send us a text Bayanai daga sassa daban-daban na Najeriya suna nuni da cewa farashin kyayyakin masarufi na ta faduwa a kasuwanni. Kafin hakan dai farashin ya yi ta tashi, har ya kai ga duk abin da mutum ya saya a yau, idan ya koma kasuwa bayan kwana biyu zai ji an ce ya tashi. Ko wadanne dalilai ne suka sa farashin kayayyakin masarufi suke ta sauka…
  continue reading
 
Loading …

Panduan Rujukan Pantas

Podcast Teratas
Dengar rancangan ini semasa anda meneroka
Main